Back to Africa Check

Hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya bata rijistar kasuwanci kyauta - kar ku bada lambar ku a yanar gizo

A TAƘAICE: Hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya bata bada sunan kasuwanci kyauta. Kuyi watsi da duk saƙon da ke buƙatar ku “ajiye” lambar ku ta WhatsApp. 

 

Hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya (CAC) ce ke da alhakin rijistar kasuwanci a ƙasa. Yanzu tana yin hakan kyauta- wannan shine abun da ke ƙunshe cikin wata da’awa da ke yawo a Facebook a watan Nuwamba 2023. 

Wani saƙon kuma na cewa: “IDAN KUNA DA SHA’AWAR RIJISTAR CAC (HUKUMAR KULA DA KAMFANONI) TA FG. KU AJIYE LAMBAR KU TA WHATSAPP ANA TA AIKIN RIJISTA YANZU KUMA KYAUTA.” 

An haɗo da hoton allon waya wato sikirinshot na abun da yayi kama da takardar rijistar sunan kasuwanci. 

An saka saƙon a nan da nan. Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun bada lambobin wayarsu a wajen yin tsokaci. 

Africa Check ta taɓa cin karo da makamanciyar da’awar cewa - gwamnatin tarayyar Najeriya ta amincewa hukumar ta yiwa kasuwanci da masu ayyukan kansu rijista kyauta - hakan ƙarya ce. 

Ko an samu wani sauyi? 

CAC_Scam

Hukumar ta ce, ayi watsi da saƙon

A ranar 7 ga watan Nuwamba, hukumar ta yi wannan gargaɗin ga ƴan Najeriya. 

“Dan Allah ku yi watsi da duk wani saƙon SMS ko WhatsApp da ke ce mu ku ku yi rijistar CAC kyauta, ba daga mu ya fito ba! Mun gode,” hukumar ta wallafa a shafin tiwita

Wasu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da suke tambayar ku bayanan da suka shafe ku, suna sa ku cin karo da abubuwa da dama. Waɗanda suka haɗa da: 

  • Waɗanda baku sani ba zasu samu damar tuntuɓar ku, har su ringa yi muku barazana.
  • Kira daga masu damfara.
  • Kai hari ta hanyar tura muku sakon sanin bayanan ku.
  • Satar bayanan sanin ku.
  • Hari ta fasahar zamantakewa, inda za’a iya yaudarar wasu ta amfani da lambar ku don samun bayanan ku.    

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.